Al’umma Na Cigaba Da Kokawa Kan Karancin Wutar Lantarki

0 100

A yayin da yanayin zafin rana ke ci gaba da zafafa da azumin watan Ramadan, al’uma na cigaba da kokawa kan karancin hasken wutar lantarki.

Yanayin zafin da rashin wutar ya jefa mutane cikin damuwa da rashin barci.

A baya gidan rediyon Sawaba ya ruwaito cewa al’umma na neman karin bayani daga kamfanonin rarraba wutar lantarki kan musabbain matsalar.

Mazauna jihohin Arewa da suka hada da jihohin Kano, Jigawa, Bauchi, da Neja da wasu da dama sun nuna damuwarsu kan matsalar wutar lantarki da aka dade ana yi a kowane wata na Ramadan.

Kamfanin Rarrabar Wutar Lantarki Shiyyar Kano da Jigawa KEDCO ya ce ƙarancin Wutar da ake fuskanta ba shi da alaƙa da zuwan Watan Azumi.

Kakakin Kamfanin Malam Sani Bala Sani ce mafi yawan ma’aikatansu Musulmai ne don haka suma ba za su so a samu ƙarancin Wutar a lokacin Azumi ba.

Akwai zarge-zarge da ke bayyana cewa, kamfanin ya karkatar da wutar ga kamfanonin ruwan sanyi dana Kankara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: