Ambaliya Ta Yi Ajalin Jami’in Tsaro da Matashi A Yobe

0 69

Ambaliya ta yi ajalin jami’in tsaro da matashi a Yobe

Mutum biyu sun rasu sakamakon ambaliyar ruwa da ruwan sama mai ƙarfi ya haddasa a wasu sassan birnin Damaturu, babban birnin Jihar Yobe.

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA) ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata.

Waɗanda suka rasu sun haɗa da Isa Haruna, mai shekara 38, jami’in tsaro da aka fi sani da Mallam Matari, da kuma Abba Kyari mai shekara 18, wanda ya nutse a unguwar Pompomari.

Hukumar ta ce ambaliyar ta afku ne a unguwannin Malari da Pompomari da maƙwabtansu bayan ruwan sama mai ƙarfi da aka yi da safiyar Litinin.

SEMA ta ce tawagarta ta ceto, tare da haɗin gwiwar Hukumar Kashe Gobara ta jihar, sun isa wurin bayan samun kiran gaggawa, amma sun tarar da mutanen biyu sun riga sun rasu.

An kai gawarwakinsu zuwa sashen kula da masu hatsari na Asibitin Kwararru na Janar Sani Abacha da ke Damaturu.

Hukumar ta shawarci mazauna yankunan da ambaliya ke yawan shafa da su yi taka-tsantsan yayin damina, tare da guje wa bi ta hanyoyin da ruwa ya mamaye ko magudanan ruwa.

Ta kuma buƙaci iyaye su hana yara zuwa koguna da rafuka da wuraren da ambaliya ta mamaye, musamman a wannan lokacin da ake hutun makaranta.

Leave A Reply

Your email address will not be published.