Sarkin Musulmi Ya Musanta Goyon Bayan Zaɓen Tinubu A 2027

0 73

Sarkin Musulmi ya musanta goyon bayan zaɓen Tinubu a 2027

Fadar Sarkin Musulmi ta ƙaryata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya buƙaci Musulman Najeriya da su sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

A wata sanarwa da Prince Bashir Adefaka ya fitar a madadin masu kula da harkokin yaɗa labarai na Sarkin Musulmi a ranar Talata, masarautar ta bayyana rahoton a matsayin na ƙarya, tana mai cewa Sarkin Musulmi uba ne ga ’yan Najeriya baki ɗaya, kuma ba ya tsoma baki a siyasar jam’iyya.

Sanarwar ta ce ƙofar Sarkin Musulmi a buɗe take ga kowa ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ko ra’ayin siyasa ba, kuma aikinsa shi ne ba da shawara da sanya albarka ga duk mai neman hakan.

Ta kuma jaddada cewa Sarkin Musulmi ba ya goyon bayan wani ɗan takara a zaɓen 2027, domin ya duƙufa ne wajen inganta zaman lafiya, haɗin kai da fahimtar juna tsakanin al’ummomin Najeriya.

Masarautar ta yi kira ga ’yan Najeriya da su yi watsi da rahoton, sannan ta buƙaci kafafen yaɗa labarai su riƙa tantance sahihancin bayanai kafin wallafawa, domin kauce wa yaɗa ruɗani da kuma jefa sarakunan gargajiya cikin siyasar jam’iyya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.