Ambaliyar ruwa ta shafi jihohi 34, ta kuma yi sanadin mutuwar mutane 321 a Najeriya

0 111

Hukumar Tattalin Arziki ta Kasa (NEC) ta bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta addabi sassan kasar nan kwanan nan ta shafi jihohi 34 da kananan hukumomi 217, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 321.

Hukumar ta NEC ta kuma ce mutane 1,374,557 abin ya shafa, inda mutane 740,743 suka rasa matsugunansu a fadin kasar.

Gwamnan jihar Anambra Farfesa Chukwuma Soludo ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa a fadar shugaban kasa dake Abuja, bayan taron hukumar zabe karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima.

Ya ce ambaliyar ta kuma yi sanadin raunata mutane 2,854 tare da lalata gidaje dubu dari 281,000 da kuma kadada dubu dari 258,000 na gonaki. Ya kuma ce majalisar ta umurci ma’aikatar albarkatun ruwa da tsaftar mahalli da ta fara gudanar da sahihin gyara ga magudanan ruwa da madatsun ruwa na Najeriya a wani mataki na dakile illar ambaliyar ruwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: