A kalla mutane 21 ne aka tabbatar sun rasu, ciki har da iyalai 12 yan gida daya, sakamakon wata ambaliya da ta afku a unguwannin Tiffin Maza da Anguwan Hausawa da ke karamar hukumar Mokwa ta jihar Neja, da daren Laraba.
Rahotanni sun ce fiye da almajirai 50 ne suka bata, yayin da ambaliyar ta lalata gidaje da dama, inda ake danganta lamarin da ruwan sama mai karfi da aka yi na tsawon dare.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja, NSEMA, ta tabbatar da adadin mutanen da suka mutu, sai dai mazauna yankin na cewa yawan mutanen da suka rasu na iya kaiwa sama da 60, musamman ma yara da mata da ambaliyar ta rutsa da su.
Daya daga cikin wadanda abin ya rutsa da su ita ce Binta, dalibar makarantar fasahar lafiya ta jihar Neja wadda ke hutu a Mokwa, kana wata mazauniyar yankin Hajiya Hassana Mokwa ta bayyana cewa 12 daga cikin ‘yan uwanta 13 sun rasu, yayin da daya tilo ya tsira amma yana kwance a asibiti, tare da sanar da cewa har wasu daliban makarantar Alkur’ani mallakin dan uwanta ma sun rasa rayukansu.