Kotu ta wanke Isa Usman daga zargin hada baki da kuma aikata fashi da makami a Jigawa

0 279

Babbar kotun jiha mai lamba 11 dake zamanta a garin Ringim ta sallami wani mai suna Isah Usman mai lakanin Niga tare da wanke shi daga zargin hada baki da kuma aikata fashi da makami.

An gabatar da Isa Usman ne a gaban kotun a ranar biyu ga watan biyu na 2020 bisa zargin aikata fashi da makami a kauyen Chaichai Tsohuwa dake karamar hukumar Dutse.

A hukuncin da ya zartar alkalin kotun mai sharia Muhammad El-Usman, ya ce masu gabatar da kara sun kasa tabbatar da zargi fiye da shakku kamar yadda doka ta yi tanadi.

Haka kuma masu gabatar da kara sun kira sheda daya ne kawai ba tare da gabatar da wata hujja ba kuma sun kasa kiran wadanda aka ce su ne wadanda aka yiwa laifin.

Saboda haka kotu ta yanke hukuncin sallama da kuma wanke wanda ake zargi daga lefukan da ake zarginsa.

Leave a Reply