An kaddamar da taron bita ta yini biyu ga Jami’an sashin kula da ayyukan gwamnati da Daraktocin tsare-tsare na jihar Jigawa

0 124

Hukumar Lura da ma’aikatan kananan hukumomi ta Jihar Jigawa tare da hadin gwiwar kungiyar (APC Progressive Institute) sun kaddamar da taron bita ta yini biyu ga Jami’an sashin kula da ayyukan gwamnati da Daraktocin tsare-tsare da bincike da kididdiga kan sanin makamar aiki na kananan hukumomin Jihar nan 27.

A jawabinsa Shugaban hukumar lura da ma’aikatan kananan hukumomi na Jiha, Alhaji Uba Bala Ringim ya ce bisa amincewar Gwamna Malam Umar Namadi ne ya baiwa hukumar damar gudanar da taron bitar domin inganta ayyukan gwamnati a matakin kananan hukumomi.

Alhaji Uba Bala Ringim ya ce daga farkon shekarar nan zuwa yanzu hukumar ta horas da ma’aikatan kananan hukumomi kusan dari biyar dabarun sanin makamar ayyukan gwamnati kala daban-daban.

shugaban haka kuma ya bukaci mahalarta bitar dasu yi amfani da ilimin da zasu koya wajen yin aiki da shi a wuraren ayyukan su domin kwalliya ta biya kudin sabulu. A nasa jawabin shugaban majalisar dokokin jihar Jigawa Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ya bukaci dukkanin shugabannin kananan hukumomin jihar nan da su rubanyya kokarin su ta hanyar kara hada kai ga ma’aikatan kananan hukumomi domin inganta ayyukan gwamnati a kananan hukumomin jihar nan.

Leave a Reply