An kammala aiyukan hanyoyin mota 24 daga cikin 26 da gwamnatin Jigawa ta gada –

0 117

Gwamnatin jihar Jigawa tace ta kammala aiyukan hanyoyin mota 24 daga cikin 26 da ta gada a 2023

Kwamishinan aiyuka da sufuri na jiha Injiniya Gambo S Malam ya sanar da hakan ta cikin shirin radio Jigawa na cikar gwamna Umar Namadi shekaru biyu da kafuwa. Ya ce sun kammala aiyukan hanyoyin mota masu nisan kilomita 256 daga cikin kilomita 340 da suka gada, kuma ragowar guda biyu suna daf da kammaluwa.

Injiniya Gambo S Malam kuma Sarkin Shanun Dutse ya ce sun bada aiyukan hanyoyi 48 kan kudi naira miliyan dubu dari uku masu nisan kilomita 977

Kwamishinan ya kuma ce an zakulo aiyukan hanyoyin ne daga kowacce shiyya ta dan majalissar dattawa guda uku da ake dasu a jihar nan.

Ya kuma ce kowane dan kwangila an bashi kudaden somin tabi na kaso 10 kuma dukkanin yan kwangila suna gudanar da aiyukansu.

A cewarsa a yanzu haka ana gudanar da aiyukan hanyoyin cikin gari a Dutse da Aujara da Fagam da Dansure da Sankara da Gandun Sarki Hadejia da sauransu.

Leave a Reply