Gwamnatin Amurka ta bukaci dukkanin bangarorin siyasa a kasar Kenya da su kaurace wa tashe-tashen hankula, sannan kuma jami’an tsaro su yi taka-tsan-tsan a yayin zanga-zanga.
Mataimakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Vedant Patel ya ce Amurka ta yi nadamar asarar rayuka da asarar dukiyoyi a zanga-zangar da aka yi a baya-bayan nan, yana mai cewa ‘yancin gudanar da zanga-zangar lumana wani bangare ne na mulkin demokradiyya.
Jagoran ‘yan adawar Kenya Raila Odinga ya yi kira da a gudanar da zanga-zanga a dukkan ranakun Litinin da Alhamis domin nuna adawa da tsadar rayuwa da kuma abin da ya kira adalcin zabe bayan zaben bara.
A wani labarin kuma, wani dan majalisar dokokin kasar Kenya ya mutu a lokacin da yake jinya a wani asibiti bayan da ya yi hatsarin babur a babban birnin kasar Nairobi.
Kullow Maalim Hassan ya kasance dan majalisar wakilai na biyu a mazabar Banisa a arewa maso gabashin Kenya.
Iyalinsa sun shaidawa kafafen yada labarai na kasar cewa, wani dan achaba ya buge dan majalisar a ranar Asabar kuma a daren jiya aka tabbatar da rasuwarsa.