Amurka Ta Mayar da Martani Kan Iƙirarin Iran Na Kama Jirgin Ruwanta

0 58

Amurka ta mayar da martani kan iƙirarin Iran na kama jirgin ruwanta

Jirgin ruwan Amurka da Iran ta ƙwaceAsalin hoton,Getty Images
Hedikwatar Rundunar Sojin Amurka da ke kula da yankin Gabas ta Tsakiya (CENTCOM) ta mayar wa BBC martani kan ikirarin da Iran ta yi na cewa ta kama wani jirgin ruwa ƙarƙashin teku maras matuƙi na Amurka a mashigin Hormuz.

A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun CENTCOM, Laftanar Kyaftin Tim Hawkins, ya ce jirgin ruwan ƙarƙashin tekun ya lalace ne fiye da kwana ɗaya da ya gabata.

Ya ce jirgin yana sintiri ne a ruwan yankin domin tallafa wa ayyukan da sojojin Amurka ke ci gaba da gudanarwa.

Hawkins ya ƙara da cewa, “jirgin tsohon samfuri wanda ba ya tattara muhimman bayanan sirri, kuma ba ya ɗauke da na’urorin radar ko na’urorin gano bayanai masu sirri.”

Ya kuma ce ayyukan sojojin Amurka a ruwan yankin na ci gaba kamar yadda aka saba.

A sa’o’in da suka gabata ne kamfanin dillancin labarai na Fars, mai alaƙa da rundunar juyin juya halin Iran, ya ba da rahoton cewa Iran ta “kama” wani jirgin ruwa ƙarƙashin teku mai fasahar zamani na Amurka.

A cewar Fars, jirgin na daga cikin sababbin jiragen ruwa marasa matuƙi masu zamani da sojojin Amurka ke amfani da su.

Kamfanin ya kuma ce an kama jirgin ne a bakin shiga mashigar Hormuz.

Leave a Reply