Sojoji Sun Kwato Makamai Bayan Daƙile Harin ’Yan Ta’adda A Borno

0 50

Sojoji sun ƙwato makamai bayan daƙile harin ’yan ta’adda a Borno

Sojojin Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation Hadin Kai (OPHK) da ke Arewa maso Gabas, sun daƙile wani kwanton ɓauna da ake zargin ’yan ta’addan Boko Haram ne suka yi musu a kan hanyar Buni Gari zuwa Buratai, a Ƙaramar Hukumar Biu ta Jihar Borno.

Mai magana da yawun rundunar, Kyaftin Mohammed Goni, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, inda ya ce sojojin 27 Task Force Brigade sun gamu da ’yan ta’addan ne yayin da suke gudanar da sintirin yau da kullum a yankin ranar Litinin, 7 ga Satumba.

Ya ce sojojin sun mayar da martani cikin gaggawa, lamarin da ya tilasta wa ’yan ta’addan janyewa babu shiri.

Goni ya ce daga bisani an tura ƙarin sojoji zuwa yankin, inda suka share wurin da aka yi kwanton ɓaunan tare da gudanar da bincike a yankin da ke kewaye da wurin.

A cewarsa, yayin aikin, sojojin sun gano tare da tarwatsa sansanonin wucin-gadi da dama da ake zargin ’yan ta’addan na amfani da su wajen fakewa da kuma shirya hare-hare.

Ya ce sojojin sun ƙwato babur guda, kekuna biyu, magazine ɗaya na AK-47, harsasai 30 ƙirar 7.62x39mm da bama-baman RPG guda biyu.

Goni ya ƙara da cewa babu wani soja da aka kashe ko ya jikkata a yayin arangamar, sai dai wasu motocin sojojin sun samu lahani.

A cewar rahotannin aikin, ɗaya daga cikin motocin sojojin masu sulken hare-haren kwanton ɓauna, wato MRAP, ta taka wani abin fashewa da aka binne a hanya, wanda ya lalata tayoyinta biyu.

Sai dai kakakin rundunar ya ce duk da lalacewar, sojojin sun ci gaba da aikin tare da kammala shi cikin nasara.

Ya ce Operation Hadin Kai za ta ci gaba da matsa wa ’yan ta’adda lamba domin hana su samun damar gudanar da ayyukansu, tare da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin Arewa maso Gabas.

Goni ya bayyana yanayin tsaro a yankin da rundunar ke da alhakin kula da shi a matsayin mai kwanciyar hankali amma ba tabbas ba, yana mai cewa sojoji na ci gaba da sintiri da sauran ayyukan tsaro domin daƙile ayyukan ’yan ta’adda.

Leave a Reply