FIFA da CAF sun dakatar da zaɓen sabbin shugabannin NFF
Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, FIFA, da takwararta ta Afirka, CAF, sun dakatar da tsarin zaɓen sabbin shugabannin Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya (NFF), tare da sanar da shirin tura tawagar haɗin gwiwa zuwa Abuja domin binciken rikicin shugabancin hukumar.
Matakin ya biyo bayan murabus ɗin shugaban NFF, Ibrahim Musa Gusau, da babban sakataren hukumar, Mohammed Sanusi, tare da wasu mambobin kwamitin zartarwa.
A wata wasiƙa mai kwanan wata 7 ga Satumba, 2026, wadda babban jami’in FIFA mai kula da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa mambobi, Elkhan Mammadov, ya aika wa Emmanuel Ikpeme, an umarci NFF da dakatar da duk wani ƙarin mataki da ya shafi tsarin zaɓen har sai an kammala tantance lamarin.
Wannan ya shafi taron zaɓen NFF da aka shirya gudanarwa ranar 27 ga Satumba a Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa, wanda NFF ta riga ta dakatar da shirye-shiryensa bayan murabus ɗin shugabannin hukumar.
FIFA da CAF sun ce a halin yanzu suna nazarin tasirin abubuwan da suka faru kan shari’a, shugabanci, gudanarwa da tsarin zaɓe na NFF.
Hukumomin biyu sun kuma jaddada cewa ba su kai ga wani matsaya ba kan batun, kuma ba su yanke shawarar matakin da za su ɗauka bayan kammala binciken ba.
Binciken zai kuma duba abubuwan da suka faru, dokoki da ƙa’idojin NFF, da kuma ra’ayoyin ɓangarorin da abin ya shafa.
FIFA da CAF sun ce bayan kammala binciken ne za su tantance ko akwai buƙatar gabatar da wasu shawarwari ga hukumomin da suka dace na FIFA da CAF.
Matakin ya biyo bayan wani taro da aka gudanar a hedikwatar FIFA da ke Zurich a ranar 1 ga Satumba, wanda ya samu halartar wakilan FIFA, CAF, NFF da gwamnatin Najeriya.
A yayin binciken, FIFA da CAF sun nemi NFF ta ci gaba da riƙe halin da ake ciki ba tare da ɗaukar wani sabon mataki kan zaɓen ba.
Haka kuma, an buƙaci Emmanuel Ikpeme ya kasance babban jami’in tuntuɓar NFF da FIFA da CAF yayin gudanar da tantancewar.
A cewar wasiƙar, tawagar haɗin gwiwar FIFA da CAF za ta ziyarci Abuja domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar ƙwallon ƙafar Najeriya, yayin da hukumomin ke neman fahimtar cikakken abin da ya haifar da rikicin shugabancin NFF.
FIFA da CAF sun kuma yi gargaɗin cewa bai kamata a riga a yi hasashen matakin da za su ɗauka ba, kasancewar har yanzu ba su kammala tantance lamarin ba.