An bukaci limaman masalatan juma-a na Karamar Hukumar Guri dasu cigaba da yin adduoi domin kara samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin da Jiha da kuma kasa baki daya.

Mataimakin shugaban majalissar dokokin jihar Alhaji Suleiman Musa Kadira ne yayi wannan kiran, inda ya jajantawa wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar rikicin Fulani da Manoma a yankin.

Yace gwamnati zata yi duk abin da ya dace domin tabatar da bin doka da oda a fadin yankin, inda kuma ya bukaci jamaar yankin dasu cigaba da zaman lafiya da junansu.

Ya kuma bukaci mazauna karamar hukumar da su kasance cikin kaunar juna da kuma tabbatar da zaman lafiya domin cigaban yankin ta kowanne fanni.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: