An bukaci Majalisa ta ware Naira biliyan 2 domin bunkasa magungunan gargajiya a Najeriya

0 532

Hukumar Cigaban Magungunan Gargajiya ta Najeriya (NNMDA) ta bukaci Majalisar Wakilai da ta amince da ware naira biliyan biyu domin bunkasa bincike da gwaje-gwaje na magungunan gargajiya a fadin kasar.

Shugaban hukumar, Farfesa Martins Emeje, ya bayyana hakan a wani taron ziyara da kwamitin Majalisar Wakilai kan bin doka ya kai hedkwatar hukumar da ke Legas, inda ya ce kudaden za su taimaka wajen samar da ayyukan yi da kuma rage dogaro da magungunan da ake shigo da su daga waje.

Ya ce Najeriya na da damar yin nasarar da China da Indiya suka samu ta fuskar asibitocin gargajiya da samar da mafita ga matsalolin lafiya ta hanyar amfani da magungunan gida.

Shugaban kwamitin, Ahmed Badau, ya bada tabbacin goyon baya, yana mai cewa wannan mataki zai taimaka wajen rage talauci, bunkasa ilimi da kiwon lafiya, da kuma karfafa tattalin arzikin kasa da bunkasar masana’antu a karkara.

Leave a Reply