An dakatar da bude makarantun kasar Malawi bayan Kwalara ta kashe mutum kusan 600 a kasar

0 136

Hukumomi a Malawi sun dakatar da buɗe makarantun Furamare da na sakandire a manyan biranen ƙasar biyu bayan ɓarkewar cutar kwalara, wadda zuwa yanzu ta yi sanadin kashe mutum 595.

Makarantu a babban birnin ƙasarLilongwe da birnin Blantyre, za su ci gaba da kasancewa a rufe na kusa akalla mako biyu zuwa sama, bayan ƙarewar hutun Kirsimeti.

Cutar ta fara ɓulla a ƙasar ne tun a watan Maris ɗin da ya gabata, inda kuma ta ci gaba da yaɗuwa a ƙasar kamar wutar daji.

Mutum 19 ne suka mutu a ranar jajiberin sabuwar shekara.

An ɗaukar cutar kwalara ne ta hanyar cin abinci ko shan ruwan da ya gurɓata da kwayoyin cutar.

Cutar kan kama ƙananan yara da manya, wadda ke haddasa gudawa mai tsanani, kuma takan kashe mutum sa’o’i ƙalilan idan ba a yi gaggawar maganinta ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: