Majalisar shura kan harkokin addinin Musulunchi ta koka bisa kisan Musulmai a kudancin Najeriya daga wasu wadanda ba Musulmai ba

0 99

Majalisar shura kan harkokin addinin Musulunchi ta koka bisa kisan Musulmai a kudu maso gabashin kasarnan daga wasu wadanda ba Musulmai ba.

Majalisar karkashin shugabancin Sarkin Musulmai, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na uku, ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen tsare rayuka da dukiyoyin Musulmai tare da hukunta wadanda suke kisan.

Majalisar ta kuma bukaci musulmai da su karbi katunansu na zabe na dindindin saboda bayanai sun nuna cewa musulmai dayawa da suka yi rijista basu karbi katunansu nasu ba.

Hakan na kunshe cikin wata takardar bayan taro da aka fitar bayan taron zaman ganawa na musamman na babban kwamitin majalisar wanda aka gudanar makon da ya gabata a Abuja.

Kwamitin yace sharrudan neman mulki sun yi sauki ta yadda ake zaben mutanen da basu cancanta ba a mukaman gwamnati.

Leave a Reply

%d bloggers like this: