Mutane 4 ne suka mutu bayan wani hatsarin sama da aka yi tsakanin wasu jirage masu saukar ungulu a gabar tekun Gold Coast na kasar Australia

0 82

Mutane 4 ne suka mutu bayan wani hatsarin sama da aka yi tsakanin wasu jirage masu saukar ungulu guda biyu a gabar tekun Gold Coast na kasar Australia.

‘Yan sandan kasar sun ce binciken farko ya nuna hatsarin ya faru ne yayin da jirgin daya ke tashi dayan kuma na shirin sauka.

‘Yan sandan sun kara da cewa wadanda suka mutu suna tafiya ne a cikin jirgi mai saukar ungulu kuma wasu fasinjoji uku na cikin mawuyacin hali.

Wani mai magana da yawun ofishin jakadancin Birtaniya ya shaidawa manema labarai cewa wasu ‘yan kasar Birtaniya biyu na daga cikin wadanda suka mutu a hatsarin.

Ya kara da cewa jami’ai na tallafawa iyalan mutanen biyu da suka mutu kuma za su ci gaba da tuntubar hukumomin yankin.

Biyar daga cikin mutane shida da ke cikin daya jirgin da ya yi saukar gaggawar, sun samu kananan raunuka.

Firayim Ministan Australia Anthony Albanese ya ce gwamnatin kasar ta yi matukar kaduwa da wannan mummunan lamari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: