An gano gawarwaki 14 yayin da wasu 6 suka bace a wani hatsarin kwale-kwale da ya afku a jihar Kebbi

0 111

An gano gawarwaki 14 yayin da wasu 6 suka bace a wani hatsarin kwale-kwale da ya afku a ranar Talata a karamar hukumar Koko/Besse a jihar Kebbi.

Sawaba ya ruwaito cewa, kwale-kwalen yana dauke da manoman shinkafa kimanin 100 zuwa garin Samanaji, dake gefen kogi, lokacin da ya kife.

Tuni aka ceto mutane 80 da ransu yayin da ake ci gaba da neman sauran mutanen shida da suka bata.

Gwamnan jihar Kebbi Atiku Abubakar Bagudu, tare da rakiyar ministan shari’a, Abubakar Malami, sun ziyarci kauyen a jiya domin jajantawa mutane dangane da hatsarin da yi musu ta’aziyya.

Atiku Bagudu ya gargadi masu sufurin kwale-kwale da su guji tafiye-tafiyen cikin dare da yin lodi fiye da kima da kuma kiyaye matakan tsaro a kowane lokaci.

Ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu da iyalansu da su yi hakurin rashi.

Gwamnan ya yabawa wadanda suka bayar da taimako wajen ceto fasinjojin jirgin da kuma ci gaba da neman wadanda suka bata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: