Jam’iyyar PDP ta kaddamar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa da kwamitin gudanarwa na kananan hukumomin Kano

0 112

Jam’iyyar PDP a jiya ta kaddamar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa da kwamitin gudanarwa na kananan hukumomi 44 na jihar Kano.

Shugaban jam’iyyar na shiyyar Arewa maso Yamma, Bello Hayatu-Gwarzo, wanda ya wakilci shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu, shine ya kaddamar da kwamitin yakin neman zaben, tawagar gudanarwa da shugabannin kwamitocin riko na shiyya-shiyya.

Ya ce kwamitin ya hada da shugabanni, mataimaka da sakatarorin kowace shiyya.

Ya bukaci kwamitocin su gudanar da ayyukansu kamar yadda ya kamata domin jam’iyyar ta samu nasara a jihar Kano.

A nasa jawabin, tsohon gwamnan jihar Kano, Mallam Ibrahim Shekarau, ya ce an zabo ‘yan kwamitin ne a tsanake saboda gudunmuwarsu da kuma biyayya ga jam’iyyar.

Mambobin kwamitin sun hada da Darakta Janar na Majalisar yakin neman zaben Atiku/Okowa, Yunusa Adamu-Dangwani, da Ibrahim Al’amin Little da kuma Umar Mai-Mansaleta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: