Hukumar Ilmi Matakin Farko ta jihar Jigawa ta gano wasu malamai basa zuwa wurin aiki na tsawon shekara da shekaru.
Daraktan wayar da kai na hukumar, Mallam Magaji Idris Bakano ya sanar da hakan ta cikin shirin radio Jigawa mai suna Jigawa A Yau.
Ya ce hukumar bisa jagorancin shugaban Hukumar Farfesa Haruna Musa ta gano cewar wasu malaman basa zuwa makaranta, wasu basa zama a jihar wasu kuma suna tura wasu domin su rike musu aiki.
Mallam Magaji Idris ya kara da cewar hakan ya sa hukumar ta dauki mataki na ladabtar da wadanda aka samu da lefin domin daukar mataki.
Yana mai cewar hukumar ta dakatar da albashin malamai fiye da dari biyu sakamakon samunsu da lefin na rashin zuwa makaranta na wata da watanni da masu bada rikon aiki.
Daraktan ya ce daukar matakai na dakatar da albashin malaman da aka samu da lefin ba sa zuwa makaranta ya taimaka wajen dakile dabiar malamai masu yin hakan.
Ya ce a yanzu haka hukumar ta bullo da tsarin zakulo hazikan malamai domin a saka musu.