Gwamnatin Jigawa ta kashe kudi sama da Naira miliyan 372 wajen gyaran kananan asibitoci guda biyar a karamar hukumar Gumel
Gwamnatin jihar Jigawa ta kashe kudi sama da naira miliyan 372 wajen gyaran kananan asibitoci guda biyar a karamar Hukumar Gumel daga cikin 72 da ake dasu a shiyyar arewa maso yamma
Kwamishinan lafiya Dr Abdullahi Muhammad Kainuwa ne ya sanar da hakan a taron gwamnati da jama-a da aka gudanar a garin Gumel
Ya ce asibitocin da aka gyara sun hadar dana Bekarya dana Uban Dawaki dana Dan Amma dana Hammado
Dr Abdullahi Kainuwa ya ce a yanzu haka za a kara gyara wasu kananan asibitocin guda uku a wannan shekara, ya kara da cewar an dauki kananan ma’aikatan lafiya na dindindin guda 43 da kuma ma’aikatan j-health 30 a karamar hukumar Gumel
Ya ce an gina cibiyar wankin koda a babban asibitin Gumel kan kudi fiye da naira miliyan 200 tare da kawo kayayyakin aiki na kimanin naira miliyan 199
A cewarsa an bada kwangilar kammala aikin gina sabon asibitin kashi na garin Gumel kan kudi naira miliyan 370 tare da kawo kayayyakin aiki na kimanin naira miliyan dari shida
Ya ce a wannan shekara an ware miliyoyin naira domin daga darajar babban asibitin garin Gumel.