Ranar 1 ga Agustan shekarar nan itace rana ta karshe ga bakin da basu sabin ta bizar su ba a Najeriya
Gwamnatin Tarayya ta saka ranar 1 ga Agustan wannan shekarar a matsayin ranar ƙarshe ga baƙin da suka wuce lokacin biza su fita ko su fuskanci hukunci mai tsauri.
Ministan Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce an buɗe wata kafa ta yanar gizo domin ba da dama ga waɗanda suka jima fiye da lokacin da aka yarda da su daidaita matsayinsu kafin a fara hukunci.
Daga watan gobe, wanda ya ƙeta zai fuskanci tara da haramta masa shigowa Najeriya har tsawon shekaru biyar zuwa goma. Gwamnatin ta ce tsarin biza ta lantarki ya samu nasara sosai, inda ya rage cin hanci da ɗaukar lokaci da yawa.