Shugaban kwamatin lura alamurran yan sanda na majalissar dattawa ta kasa , Sanata Ahmad Abdulhamid yace , hukumar lura da harkokin yan sanda ta kasa ta samu sahalewar daukar kuratan yansanda dubu talatin a wannan shekara.
Sanatan ya bayyana hakan ne a lokacin ganawa da manema labarai a ofishinsa.
Ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kuma sake amincewa hukumar daukar kuratan yansanda dubu talatin a duk shekara domin cike gibin da ake da shi a aikin dan sanda.
Shugaban kwamitin kuma wakilin mazabar Jigawa ta gabas a majalissar dattawa ta kasa , ya bukaci matasa masu shaawar aikin dan sanda dasu rinka bibiyar shafin sadarwa na hukumar domin sanin lokacin fara daukar sabbin yan sandan.