An gargadi direbobin da ke yin karan tsaye ga ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a yayin da suke tuki

0 162

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi,  a yau, ya gargadi direbobin da ke yin karan tsaye ga ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a yayin gudanar da ayyukansu da su guji aikata hakan.

Ya bayyana hakan ne a yau Juma’a a cikin wani faifan bidiyo mai tsawon mintuna hudu da dakika 27 da aka wallafa a shafin yanar gizo na rundunar ‘yan sandan Najeriya.

Ya kara da cewa direbobin da suka zabi su yi fada ko sa’in sa da jami’an tsaro suna aikata babban kuskure kuma zasu fuskanci hukunci mai tsanani.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan ya ce a kowane irin hali kamata yayi direbobi subi umurnin jami’an tsaro ko da kuwa zasu dauke su ne izuwa ofisoshin su ko kuma zasu dauki ababen hawan su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: