An cafke wasu fitattun mutane da ake zargi da hannu wajen aikata fashi da makami

0 140

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta bayyana cewa ta cafke wasu fitattun mutane da ake zargin suna da hannu wajen aikata fashi da makami.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Muhammad Dalijan ne ya bayyana hakan a lokacin da yake karbar bakuncin shugaban sashin yaki da ta’addanci a ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai yaki da miyagun kwayoyi da laifuka, Thomas Parker.

A cewarsa, an kama wani dan majalisar dokokin jihar a yanzu, da hakimi, da kuma tsohon shugaban karamar hukuma.

Amma bai fadi sunayen wadanda ake zargin ba.

Dalijan ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta taimaka wajen kafa dakin gwaje-gwaje na bincike da kuma taimakawa wajen karfafa rundunar a fannin horarwa da bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: