Jami’an Hukumar Hisbah ta Jihar Kebbi sun kama wani mutum da ake zargi da yin mu’amala da wata matar aure a unguwar Badariya da ke jihar.
Rahotanni sun ce mazauna yankin ne suka kai ƙorafi ga hukumar bayan sun zargi akwai alaƙa ta musamman tsakanin matar da mutumin.
Bayan gudanar da bincike, jami’an Hisbah sun gano mutumin a ɓoye cikin wata ƙatuwar jakar “Ghana Must Go” a ɗakin matar, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a unguwar. Daga suka hankada keyarsa uwa ofishinsu domin daukar matakin shari’a.