Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC), ta samu nasara a kotu wajen kwace wani jirgin sama na alfarma kirar Hawker 800XP mai lamba 5N-AMK, bisa zargin alaƙarsa da badakalar kuɗi da kuma wanke kuɗaɗe da suka shafi aikin samar da lantarki na Maiduguri, jihar Borno.
A cewar EFCC, ana zargin Abdulsalam Mustapha Kachallah, tsohon shugaban hukumar samar da wutar lantarki a karkara a jihar Borno, da amfani da matsayinsa wajen samun bayanan kwangila da kuma karɓar kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba.
Hukumar ta bayyana cewa binciken da take gudanarwa ya gano alaƙar jirgin saman da wasu kuɗaɗen da ake zargin an samu ta haramtacciyar hanya daga aikin.
Kotun ta amince da bukatar EFCC na ƙwace jirgin saman yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.