ASUU Ta Gargadi Gwamnati Kan Yiwuwar Sake Shiga Yajin Aiki

0 67

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya, ASUU, ta yi barazanar sake shiga yajin aiki sakamakon abin da ta bayyana a matsayin gazawar gwamnatin tarayya wajen cika yarjejeniyar da aka cimma a shekarar 2025.

Ƙungiyar ta bayyana cewa gwamnatin ta kasa aiwatar da muhimman alkawuran da suka shafi biyan haƙƙoƙin malamai, inganta walwalar ma’aikata da kuma bunƙasa harkokin jami’o’in gwamnati a faɗin ƙasar nan.

ASUU ta kuma yi gargadin cewa idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba domin warware matsalolin da ake fuskanta, hakan na iya janyo tsaikon karatu a jami’o’in Najeriya.

Kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta mutunta yarjejeniyoyin da aka cimma domin kaucewa sake fadawa rikicin yajin aikin da kan shafi ɗalibai da tsarin ilimi baki ɗaya.

Leave a Reply