Kotu Za Ta Yanke Hukunci Kan Takarar Jonathan A 2027

0 57

Kotun Tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 26 ga watan Mayu domin yanke hukunci kan ƙarar da ke neman hana tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

A zaman kotun na baya-bayan nan, lauyoyin Jonathan tare da Ministan Shari’a sun buƙaci kotun da ta yi watsi da ƙarar, suna mai cewa ba ta da tushe a doka. Haka kuma, sun nemi alkalin da ke sauraron shari’ar ya janye daga ci gaba da sauraron karar.

Masu shigar da ƙarar na neman kotu ta hana Jonathan sake neman kujerar shugaban ƙasa, suna danganta hakan da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Najeriya kan wa’adin mulki.

Bayan sauraron dukkan ɓangarorin da ke cikin shari’ar, kotun ta ɗage zaman zuwa ranar 26 ga watan Mayu domin yanke hukunci kan buƙatun da aka gabatar.

Leave a Reply