’Yan Sanda Sun Cafke Masu Garkuwa Da Dattijo Domin Karɓar Kuɗin Fansa a Kaduna

0 62

’Yan Sanda sun cafke wasu mutane biyu da ake zargi da haɗa baki wajen sace wani dattijo a jihar Kaduna domin neman kuɗin fansa, tare da ƙwato bindiga ƙirar AK-47.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labaran Rundunar, Anthony Okon Placid ya fitar ranar Talata 19 ga Mayu, 2026.

Sanarwar ta bayyana cewa bincike ya nuna Yusuf Rabo, ɗan Alhaji Rabo Jelani, ya haɗa kai da Musa Adamu da Ali Haruna — wanda shi ne jikan dattijon — domin sace mahaifinsa bisa zargin cewa yana da dukiya da dabbobi masu yawa.

Binciken ya kuma gano cewa an sace dattijon har sau biyu, inda aka karɓi kuɗin fansa naira miliyan biyu a karon farko, sannan naira miliyan huɗu da dubu ɗari biyar a karo na biyu.

Rundunar ta ce ana ci gaba da neman Ali Haruna, jikan dattijon da ake zargi da hannu a lamarin.

Kazalika, rundunar ta jaddada aniyarta na ci gaba da yaƙi da masu garkuwa da mutane da ’yan fashi a faɗin ƙasar nan.

Leave a Reply