APCn Bauchi: Tuggar, Bala Wunti da wasu biyar za su fafata a fidda gwanin APC a jihar Bauchi

0 145

Jam’iyyar APC ta amince da sunayen wasu ’yan takara bakwai domin shiga zaɓen fidda gwanin kujerar gwamnan Jihar Bauchi na shekarar 2027.

A cikin waɗanda aka tantance akwai Ministan Harkokin Waje, Yusuf Maitama Tuggar, da tsohon babban jami’in NNPCL NUIMS, Bala Wunti.

Sauran waɗanda aka tantance sun haɗa da Nura Manu Soro, M. A. Abubakar, Kabir Baba Maaji, Baba Abubakar Suleiman da Yakubu Yakubu Abdullahi.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa jam’iyyar ba ta tantance Sanata Shehu Buba Umar ba, inda wasu majiyoyi suka danganta hakan da wasu matsaloli da ba a bayyana ba.

Majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa APC na kallon jihar Bauchi a matsayin muhimmiyar jiha a zaɓen 2027, saboda haka take ƙoƙarin fitar da ’yan takara masu ƙarfi da za su iya fafatawa da sauran jam’iyyu.

Ana sa ran wannan mataki zai sauya yanayin siyasar jihar Bauchi gabanin babban zaɓen 2027, yayin da Tuggar da Bala Wunti ke ci gaba da fitowa a matsayin manyan ’yan takara a jam’iyyar APC.

Leave a Reply