An kama wata mata bisa zargin satar yarinya ’yar shekaru uku a garin Minna na Jihar Neja

0 270

’Yan sandan sun kama wata mata mai shekara 51 kan zargin satar wata yarinya ’yar shekara uku a garin Minna na Jihar Neja.

Da yake gabatar da wadda ake zargin, kakakin ’yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun, ya ce a ranar 25 ga watan Oktoba aka ganta a “unguwar Keteren-Gwari tana kokarin shiga motar haya domin tafiya da wata yarinya ’yar shekara uku da ake zargin an sace ta.

Ya ce ‘yan sanda da ke aiki a yankin Tudun-Wada sun kama wadda ake zargin tare da yarinyar kuma da suka yi mata tambayoyi, ta amsa cewar ta sato yarinyar ne daga wani gida a unguwar Tudun-Natsira.

Ta kara da cewa ta yi niyyar sayar da ita ga wata mata a garin Nnewi da ke Jihar Anambra, wadda ta ba ta kwangilar a kan kudi N530,000.

Ta ce ta karbi wasu N230,000 daga cikin kudin kafin ta kawo yarinyar da ta sace. Abiodun, ya ce an mayar da yarinyar ga iyayenta kuma ana ci gaba da kokarin cafke daya matar da ke Anambra.

Leave a Reply

%d bloggers like this: