Hukumar Sadarwa ta kasa (NCC), ta kara wa’adin hada layukan waya da Lambar Shaidar dan Ƙasa (NIN) zuwa ranar 14 ga watan Satumba, 2024.
Hukumar ta bayyana cewa an riga an haɗa layuka sama da miliyan 153 da lambar NIN, inda aka samu nasarar kashi 96%, wanda ya karu daga kashi 69.7% a watan Janairun 2024.
NCC ta jaddada muhimmancin kammala haɗa layukan waya da lambar NIN don karfafa tsaro a harkokin yanar gizo da hana zamba, tare da kira ga wadanda ba su hada layukansu ba da su yi hakan kafin sabon wa’adin ya cika.
Don magance wannan matsalar, NCC tana aiki tare da hukumomin tsaro don kawar da sayar da layukan da aka riga aka yi wa rajista domin kare tsaron kasa. Hukumar ta kuma gargadi jama’a cewa saye ko sayar da layukan da aka yi wa rajista laifi ne, tare da jan kunnen al’umma su kai rahoton duk wanda suka samu na aikata hakan ga hukumar.