An kashe ‘yan bindiga sama da 40 a Arewa maso Yamma

0 92

Mukaddashin Daraktan Tsaro na Ayyukan Kafafen Yada Labarai, Birgediya Janar Benard Onyeuko, wanda ya bayyana hakan, ya ce sojoji sun kai samamen ne a dazuzzukan da ke tsakanin jihohin Sokoto da Kaduna.

Ya sanar da haka a helkwatar tsaro dake Abuja, yayin da yake bayar da bahasin ayyukan sojoji a inda ake yaki, tsakanin ranar 1 ga watan Oktoba zuwa 13 ga watan na Oktoba.

Babban jami’in sojin, wanda kuma ya bayyana yadda aka lalata gine-gine da dama wadanda suka kasance sansanin ‘yan fashin, ya yi bayanin cewa ayyukan sun zama tilas domin tabbatar da cewa an kawar da barazanar tsaro a duk fadin kasarnan.

A cewarsa, a cikin makonni biyun da suka gabata, an kaddamar da hare-hare da yawa a maboyar ‘yan bindiga da ke wurare daban-daban.

Leave a Reply

%d bloggers like this: