Mayakan Boko Haram da na ISWAP dubu 133 da 243 da iyalansu sun mika wuya ga sojoji a Arewa maso Gabas

0 83

Helkwatar tsaro ta ce ya zuwa yanzu, mayakan Boko Haram da na ISWAP dubu 133 da 243 da iyalansu sun mika wuya ga sojoji a Arewa maso Gabas.

Mukaddashin Daraktan Tsaro na Ayyukan Kafafen Yada Labarai, Birgediya Janar Bernard Onyeuko, ya bayyana hakan yau a Abuja yayin da yake bayar da bayanai kan ayyukan sojoji a fadin kasarnan.

A cewar Onyeuko, mayakan da suka mika wuya da iyalansu sun hada da maza dubu 3 da 243, da mata dubu 3 da 868 da kuma yara dubu 6 da 234.

Ya ce sojojin Operation Hadin Kai suna ci gaba da barin wuta babu kakkautawa a Arewa maso Gabas kuma hakan ya bayar da sakamako mai kyau cikin makonni biyun da suka gabata.

Ya ce jerin ayyukan sojin kasa da na sama da aka gudanar a wurare daban-daban a jihoshin na Arewa maso Gabas ya rage karfin ayyukan masu tayar da kayar baya inda aka kashe da yawa daga cikinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: