Majalisar wakilai ta zartar da kasafin kudin badi na naira tiriliyan 16 da miliyan dubu 390 domin karatu na biyu

0 104

Majalisar wakilai ta zartar da kasafin kudin badi na naira tiriliyan 16 da miliyan dubu 390 domin karatu na biyu.

Wannan ya biyo bayan kammala muhawara kan manyan ka’idojin kasafin kudin.

Majalisar Dattawa, ita ma ta zartar da Dokar Kasafin Kudin na badi domin karatu na biyu a jiya, bayan sama da awa daya ana muhawara kan manyan ka’idojinsa.

A makon da ya gabata, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kudirin kasafin kudi na naira tiriliyan 16 da miliyan dubu 390 domin shekarar 2022 mai zuwa.

Shugaban kasar ya ce daga cikin jimlar kasafin kudin da aka gabatar wa Gwamnatin Tarayya na shekarar 2022, za a kashe naira tiriliyan 6 da miliyan dubu 830 na harkokin da ba na biyan bashi ba, sai naira tiriliyan 4 da miliyan dubu 110 domin biyan albashin ma’aikata da naira tiriliyan 5 da miliyan dubu 350 na manyan ayyuka da naira tiriliyan 3 da miliyan dubu 610 na rage basussuka, da sauransu.

Kasafin kudin na da gibin naira tiriliyan 6 da miliyan dubu 260, wanda sai an ciyo bashi za a cike shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: