Kotu a jihar Kano ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan wani magidanci da ya kashe matarsa

0 103

Wata kotu a jihar Kano ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan wani magidanci, mai suna Aminu Inuwa, da aka samu da laifin kashe matarsa, Safara’u Mamman.

Mista Aminu Inuwa wanda ba a bayyana shekarunsa ba, mazaunin unguwar Gwazaye ce da ke Dorayi Babba a Kano.

Mai shari’a Usman Na’abba ya ce kotu ta tabbatar da cewa Inuwa ya aikata wannan laifi.

Mutumin da aka yankewa wannan hukunci ya yi wa matarsa yankan rago sakamakon musu da ya shiga tsakaninsu, sannan ya binneta a wani daki da ba a karasa gininsa ba a cikin gidan da suke zama.

Mai gabatar da kara Barista Lamido Soron Dinki ya gabatar mutane uku da wasu shaidu shida da suka tabbatar da aikata wannan laifi.

Magidancin dai ya musanta aikata wannan laifin.

Haka kuma mutumin da ake zargin ya gabatar da shedar mutum 1 domin tabbatar da cewa bai amsa laifin ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: