An Kori Jami’an ‘Yan Sanda Uku Tare Da Ragewa Wasu 5 Mukami

0 81

Hukumar kula da ‘yan sanda ta amince da korar jami’an ‘yan sanda uku tare da ragewa wasu 5 mukami.

Shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na hukumar, Ikechukwu Ani, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa jiya a Abuja, inda ya ce an tsawatarwa wasu jami’ai 20 da suka yi laifi.

Ya ce jami’an da aka kora sun hada da mataimakan sufiritandan uku, yayin da wadanda aka ragewa mukamin suka hada da mataimakin kwamishina, da babban sufeton ‘yan sanda, da masu mukamin sufeto biyu da mataimakin sufeto daya.

Ikechukwu Ani ya ce wadanda aka tsawatarwar mai tsanani sun hada da mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, da babban sufeton ‘yan sanda, da masu mukamin sufeto hudu, da mukaddashin sufiritanda biyu da mataimakan sufiritanda 12.

Ya ce an yanke shawarar hakan ne a yayin babban taron hukumar karo na 20, wanda shugaban hukumar Dakta Solomon Arase ya jagoranta. Ikechukwu Ani ya kara da cewa an amince da karin girma ga manyan ma’aikatan hukumar su 109 yayin taron.

Leave a Reply

%d bloggers like this: