Za’a Bayar Da $1.2M Domin Kwaso Yan Najeriya Daga Sudan

0 56

A wani labarin kuma, majalisar ta amince da bayar da dala miliyan 1 da dubu 200 domin kwaso ‘yan Najeriya da suka makale a kasar Sudan da yaki ya daidaita.

Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa game da sakamakon taron majalisar wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta jiya a Abuja.

A cewar Geoffrey Onyeama, za a kashe kudaden ne wajen daukar hayar motocin bas na alfarma da za suyi jigilar ‘yan Najeriya da suka makale daga Khartoum babban birnin Sudan zuwa kasar Masar, inda daga nan za a kawo su Najeriya ta jirgin sama.

Shima da yake tsokaci kan lamarin, karamin ministan harkokin waje, Zubairu Dada, ya bayyana cewa babu wani dan Najeriya da ya rasa ransa a kasar Sudan tun bayan barkewar rikici a ranar 15 ga watan Afrilu. Zubairu Dada ya kara da cewa gwamnati ta kuma tanadi hanyoyin tsaro da jigilar ‘yan Najeriya zuwa kan iyakar kasar Masar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: