Majalisar Zartarwa Ta Tarayya Ta Amince Da Shirin Dabbaka Kare Hakkin ‘Yan Najeriya Na Shekarar 2022 Zuwa 2026

0 73

Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da shirin dabbaka kare hakkin ‘yan Najeriya na shekarar 2022 zuwa 2026.

Babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a Abubakar Malami ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan taron majalisar na mako-mako wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta, jiya a Abuja.

Masu ruwa da tsaki a ma’aikatu da sassa da hukumomin gwamnati ne suka tsara shirin.

Ya ce amincewar da gwamnatin Buhari ta yi ya biyo bayan hukuncin da hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa ta yanke tare da biyan diyyar Naira miliyan 135 ga wadanda suka jikkata da kuma ‘yan uwan wadanda aka kashe a ranar 18 ga Satumba, 2013 a Apo, Abuja.

Abubakar Malami ya kuma ce rahoton kwamitin kare ‘yan jarida, ya kuma bayyana Najeriya a matsayin kasa daya tilo a nahiyar Afirka da ta cika dukkan sharruddan kare hakkin ‘yan jarida.

Leave a Reply

%d bloggers like this: