Jami’an Amurka sun ce Taliban da ke mulkin Afghanistan Ta Kashe Wani Jigon Kungiyar IS

0 83

Jami’an Amurka sun ce Taliban da ke mulkin Afghanistan ta kashe wani jigon kungiyar IS da ake zaton ya shirya mummunan harin bam a filin jirgin saman Kabul da ke Afganistan a shekara ta 2021.

Harin da aka kai a watan Agusta ya kashe fararen hula 170 da sojojin Amurka 13 a lokacin da mutane ke kokarin ficewa daga kasar a daidai lokacin da ‘yan Taliban suka karbe iko.

An kashe jigon na IS makonnin da suka gabata amma an dauki lokaci kafin a tabbatar da mutuwarsa. Sai dai ba a bayyana sunansa ba.

Jami’an Amurka sun ce ta hanyar tattara bayanan sirri da kuma sanya ido a yankin sun tabbatar da cewa mutumin ya mutu, ko da yake ba su bayar da karin bayani kan yadda suka gano cewa shi ne ke da alhakin kai harin ba.

A cewar wani rahoto na jaridar New York Times, Amurka ta samu labarin mutuwar mutumin a farkon watan Afrilu. Babu tabbas ko Taliban ce ta kai masa hari ko kuma an kashe shi yayin da ake ci gaba da gwabza fada tsakanin kungiyar IS da Taliban. Amurka ta fara sanar da iyalan sojojin da aka kashe game da mutuwar shugaban na IS.

Leave a Reply

%d bloggers like this: