An lalata kayayyaki na miliyoyin naira bayan barkewar zanga-zangar da aka yi kan ‘yan Arewa a birnin Fatakwal, babban birnin Jihar Rivers, sakamakon kisan wani mazaunin yankin Igwuruta da ake zargin wani mai sana’ar babur ɗin haya ne ya aikata.
Rahotanni sun ce mamacin, Nchelem Samuel Festus, ɗan asalin Igwuruta, ana zarginsa da satar wani babur daga shagon wasu ‘yan Arewa, inda yayin da ake ƙoƙarin kwato babur ɗin aka ce an soke shi da wuka, lamarin da ya janyo rasuwarsa daga baya.
Lamarin da ya faru a ranar 10 ga watan Fabrairu ya tayar da zanga-zanga, inda masu zanga-zangar suka zargi masu sana’ar babur daga Arewa da hannu a mutuwar Festus, tare da ƙara zargin wasu ‘yan Arewa da aikata laifuka kamar fyade da garkuwa da mutane.
Rikicin ya ƙara tsananta ne lokacin da matasa suka tare hanyar zuwa filin jirgin sama na Fatakwal, suna neman a haramta wa masu sana’ar babur daga Arewa aiki a yankin, tare da rufe wuraren ajiye tarkace da kuma kama waɗanda ake zargi da hannu a kisan.
Masu zanga-zangar sun bai wa jami’an tsaro wa’adin sa’o’i 48 su ɗauki mataki, suna mai gargadin cewa rashin ɗaukar mataki na iya tilasta musu kare rayukansu da dukiyoyinsu, duk da cewa sun ce za su yi hakan ne cikin bin doka.
Tashin hankalin ya ƙara ƙamari a ranar Asabar bayan wani mai mai suna Zakara Afaaruwu ya soki wani ɗan kasuwa daga Jihar Benue, Higightor Wenem, har lahira bayan takaddama kan wurin kasuwanci a kasuwar Oil Mill, lamarin da ya kara rura wutar fadan da hari kan ‘yan kasuwa ‘yan Arewa, inda aka lalata shaguna tare da kwashe kayayyaki.
Shugaban al’ummar Hausawa na Jihar Rivers, Musa Saidu, ya yi kira da a kwantar da hankali, yana mai gargadin cewa bai kamata a ɗora laifin mutum ɗaya kan wata ƙabila gaba ɗaya ba, yayin da rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da kama wanda ake zargi da aikata kisan, tare da cewa ana ci gaba da bincike, kuma shugabannin ƙaramar hukuma sun sanar da takaita zirga-zirgar babura da daddare domin dawo da zaman lafiya da hana sake aukuwar irin wannan rikici.