An nada shugaban tuntuba da kula da ayyukan hukumar kula da Almajirai ta Jihar Jigawa

0 141

Hukumar kula da Almajirai da yaran da basa zuwa makaranta ta kasa ta nada, Malam Abdullahi Yunusa a matsayin shugaban tuntuba da kula da ayyukan hukumar a Jihar Jigawa.

A sanarwar da Sakataren zartarwa na hukumar, Dokta Muhammad Sani Idris ya fitar, ta ce nadin ya biyo bayan gudunmawar da yake baiwa tawagar tuntuba ta hukumar a Jihar Jigawa.

Sanarwar tayi bayanin cewa hukumar tana ta yakinin cewa, Malam Abdullahi Yunusa zai bada gagarumar gudunmawa wajen samun nasarar ayyukan hukumar.

Sanarwar ta kara da cewa, hukumar ta dukufa wajen kaiwa ziyarar tuntuba, inda ta zabi jihohi takwas wajen gudanar da wannan aiki a matsayin gwaji, ciki harda Jihar Jigawa.

Sauran Jihohin da aka zaba sun hadar da Borno da Cross River da Imo da Kano da Yobe da Ogun da kuma Lagos. Rahotanni sun ce tuni hukumar ta kaddamar da shugabannin kwamitocin tuntubar na Jihohi a ranar 26 ga wannan wata na Mayu a helkwatar hukumar dake Abuja.

Leave a Reply