Gwamnatin jihar Jigawa tace ta biya kudaden tallafin karatu fiye da naira miliyan dubu shida da miliyan dari takwas ga dalibai fiye da dubu talatin a shekara ta 2024
Babban mataimaki na musamman ga gwamnan jiha kan harkokin dalibai Salisu Muhammad Seeker ya sanar da haka ta cikin shirin radio Jigawa na musamman na cikar gwamnati shekaru biyu akan karagar mulki
Ya ce gwamna Umar Namadi ya kara tallafin karatun dalibai da kaso dari
Salisu Muhammad Seeker yana mai cewar gwamnati ta biya dukkannin basukan tallafin karatun dalibai Jigawa dake karatu a ciki da kuma wajen jihar nan
Ya kara da cewar gwamnatin jiha ta sake fasalin biyan tallafin karatun dalibai , inda a yanzu ake biyan tallafin karatu na dalibai a kowacce shekara
Babban mataimakin na musamman ga gwamna ya ce ofishinsa yana tallafawa karatun marayu da na masu karamin karfi yayinda suka raba kayayyakin sawa na makaranta ga dalibai dubu talatin tare da raba littatafai da sauran kayayyakin karatu A cewarsa sun sayawa dalibai takardun rubuta JAMB yayinda suka dauki nauyin karatun dalibai fiye da dari hudu.