Shugaban kungiyar Fulani ta Fulbe Joda Jam na Jihar Jigawa Alhaji Isa Bello Gwaram ya bukaci Fulani su kara hada kai, kuma su cigaba da marawa gwamnati baya domin amfana da tsare-tsaren kyautatat rayuwar al’umma da ta bullo da su.
Da yake ganawa da wakilinmu, Alhaji Isa Bello ya ce Gwamna Malam Umar Namadi yana kula da rayuwar al’ummar Fulani ta kowanne fanni, don haka ya zama wajibi a garesu su kara baiwa Gwamnati hadin kai domin cimma burin da ta sag aba.
Shugaban kungiyar ya kuma bukaci makiyaya su zauna lafiya da manoma domin bunkasar tattalin arzikin su.
Shugaban kungiyar ta Fulbe Joda Jam ya yabawa al’ummar Fulani bias hadin kai da goyan baya da suke baiwa shugabancin kungiyar, lamarin da ya kara wanzar da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin manoma da Fulani makiyaya.
Haka kuma, ya jaddada kudirin kungiyar na ciga da kare yan cin al’ummar Fulani ta kowanne fanni.