Kungiyar MRHC ta bawa mata masu juna biyu 7,883 damar samun kulawa da lafiyar su a jihar Legas

0 152

Shirin kula da lafiyar uwaye da jarirai da kungiyar Maternal and Reproductive Health Collective (MRHC) ke jagoranta ya bai wa mata masu juna biyu 7,883 damar samun kulawar lafiya kafin haihuwa da kuma agajin gaggawa a ƙananan hukumomi 12 na jihar Legas.

An aiwatar da shirin mai suna MamaBase tsakanin watan Oktoba 2023 zuwa Satumba 2024, inda aka maida hankali kan kyautata lafiyar mata a al’ummomin da ke fama da rashin isassun cibiyoyin kiwon lafiya, ta hanyar haɗa su da asibitoci da kuma samar da hidima kyauta.

A wani taron manema labarai a Legas, mukaddashin daraktan gudanarwa na kungiyar, Olajumoke Oke, ta bayyana cewa an samu haihuwa lafiya guda 7,467, tare da rage yawan mace-macen mata masu juna biyu zuwa kashi 123 cikin 100,000—wanda ke ƙasa da matsakaicin ƙimar ƙasa baki ɗaya. Ta ce wannan nasara da aka samu a ƙananan hukumomi kamar su Epe, Eti-Osa, Ibeju-Lekki da Mushin na nuna cewa tsare-tsare na musamman na iya haɓaka lafiyar mata a yankunan da ke fama da ƙarancin albarkatu.

Leave a Reply