An Raba Naira Biliyan 714 Da Miliyan 629 A Matsayin Kudaden Tarayya Na Watan Maris

0 53

Kwamitin rabon arzikin kasa a jiya ya raba naira biliyan 714 da miliyan 629 ga matakai uku na gwamnati a Abuja a matsayin kudaden tarayya na watan Maris.

Wannan yana kunshe ne a cikin sanarwar da aka fitar a karshen taron kwamitin na watan Afrilu.

Kakakin kwamitin, Stephen Kilebi, ya bayyana cewa kudaden da aka raba sun hada da ginshikin kudaden shiga na naira biliyan 497 da miliyan 448, da harajin kayayyaki na VAT na Naira biliyan 202 da miliyan 693, da kuma harajin kudaden da ake caji a bankuna na naira biliyan 14 da miliyan 488.

Daga cikin kudaden, gwamnatin tarayya ta samu naira biliyan 276 da miliyan 141; jihohi 36 na tarayya sun samu naira biliyan 232 da miliyan 129, yayin da kananan hukumomi 774 suka samu Naira biliyan 171 da miliyan 257. Jihohin da ake hako mai sun samu karin Naira biliyan 35 da miliyan 102 a matsayin kashi 13 cikin 100 na Asusun Hako Man Fetur.

Leave a Reply

%d bloggers like this: