An Bayar Da Izinin Zama ‘Yan Najeriya Ga Mutane 385 Da Suka Nema Kuma Suka Cika Sharudda

0 69

Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da bayar da izinin zama ‘yan Najeriya ga mutane 385 da suka nema kuma suka cika sharudda.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a jiya yayin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.

A cewar ministar, nau’ikan takardar shaidar zama dan kasa da ake baiwa mutanen sune na haihuwa a kasa da kuma na rijista.

Ya ce majalisar ta kuma amince da kasuwancin aikin samar da tsarin gargadi da gano gobara na kasa wanda ya kunshi tsarin ceto rayuka da sadarwa da sanya ido da kuma aikawa da sako kai tsaye. A cewarsa, aikin zai kasance akan tsarin hadin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: