Indiya Zata Maye Gurbin China A Matsayin Kasa Mafi Yawan Jama’a A Duniya

0 86

Kididdigar da asusun kula da yawan jama’a na Majalisar Dinkin Duniya ya yi ya nuna cewa nan ba da jimawa ba kasar Indiya za ta maye gurbin kasar China a matsayin kasa mafi yawan jama’a a duniya.
Kamar yadda yazo a bayanai daga Rahoton Yawan Jama’a na Duniya da aka buga a yau, zuwa tsakiyar shekarar 2023, kasar Indiya za ta sami mutane kimanin miliyan 3 fiye da China.
A cewar rahoton, Indiya za ta kasance tana da mutane biliyan 1 da miliyan 428, yayin da China zata kasance tana da mutane biliyan 1 da miliyan 425.
Ana sa ran yawan mutanen duniya zai kai biliyan 8 da miliyan 45.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce ba zai yiwu a tantance ainihin ranar da kasar Indiya za ta wuce kasar China ba, idan aka yi la’akari da bayanan da aka samu.
Alal misali a India, kidayar baya-bayan nan an yi ta ne a cikin shekarar 2011 kuma sabon aikin kidayar da ya kamata a gudanar a shekarar 2021, an daga shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: