‘Yan Sanda Sun Kubutar Da Mutane 8 Da Akayi Garkuwa Dasu A Jihar Binuwai

0 83

Rundunar ‘yan sandan jihar Binuwai ta ce jami’anta sun kubutar da dukkan mutane takwas din da aka yi garkuwa da su ba tare da sun ji rauni ba a kauyen Owukpa da ke karamar hukumar Ogbadibo a jihar.
An bayar da labarin cewa an yi garkuwa da mutanen ne da yammacin ranar Lahadi a kan hanyar Atamka zuwa Ugbugbu a kauyen Owukpa a lokacin da suke dawowa daga kasuwar kauye.
Sai dai mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda a jihar, Catherine Anene, a jiya ta tabbatar da cewa an yi garkuwa da mutanen ne a hanyarsu ta zuwa gona.
Catherine Anene a wani sabon labarin da ta fitar a yau tace an samu nasarar ceto su.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan a wani labarin na daban, ta tabbatar da ceto dukkan mutanen takwas din da lamarin ya rutsa da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: